Saturday, 7 October 2017

Kaico! Yadda wani Ɗansanda ya halaka wani mutumi saboda an hana shi cin hancin naira 100

Wasu Fasinjoji sun kashe Dansandan sakamakon wata takaddama data kaure tsakaninsa direbansu da shi a tashar mota, kamar yadda rahoton jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Wannan mummunan lamari ya auku ne a ranar Alhamis 5 ga watan Oktoba a kauyen Wuro-Dole dake karamar hukumar Girei na jihar Adamawa, inda dansandan ya bukaci direban ya bashi kudi.

Jami’in Dansandan ya nemi direban motar ya bashi Naira 100 a matsayin cin hanci, inda shi kuma direban ya mika masa Naira 50, daga nan fa sai suka shiga cacar baki, suna hada ma juna magana.


Majiyar Arewarmu.com ta ruwaito ana cikin haka ne, sai Fasinjojin motar suka sa baki, suna yi ma dansandan fada, shi kuwa cikin bacin rai ya bude wuta, inda ya kashe fasinjan motar guda daya, ya ji ma daya ciwo.

Wani direban mota da akayi abin a gabansa yace “Ganin ya kashe mutum daya, sai dansandan ya yar da bindigarsa ya ruga, amma Fasinjar suka ce da wa Allah ya hada mu, in ba kai ba, suka kuwa kama shi, suka kashe shi da duwatsu".

Sai dai tuni Yansanda suka dauke gawar dansandan, kamar yadda Kaakakin Yansandan jihar ya tabbatar da faruwar lamarin.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: