Tuesday, 21 November 2017

Ana wata ga wata: Wasu Malaman Makaranta sun kara fadi jarrabawar koyarwa

Mun samu labari cewa wasu Malaman Makaranta a Jihar Legas sun fadi jarrabawar koyarwa da Hukumar rajistar Malamai ta kasa ta gudanar. Daga ciki har da wani mai PhD da kuma masu Digiri na 2 har 282 sannan masu Digiri da NCE.
Malamai 51 ne su ka gaza cin jarrabawar da Hukumar nan ta TRCN mai rajistar Malaman Najeriya ta gudanar da ake kira PQE. A cikin Malamai sama da 400 da su ka zauna jarrabawar an samu wasu 51 da ba su samu nasara ba.

Gbolohan Enilobo wanda shi ne Shugaban Hukumar na Yankin Legas ya bayyanawa manema labarai wannan a jiya Litinin. Enilobo yace Malaman da su ka fadi sun samu matsalar amfani ne da na’ura mai kwakwalwa ta zamani.

Idan ba a manta ba a tsakiyar watan jiya na Oktoba ne aka yi wa Malaman wannan jarrabawa. Za a ba wadanda su ka fadi dama har sau 3 domin su kara jarraba sa’a wanda idan abin ya gagara bayan nan za a sallame su watau ba su ba malanta.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: