Babban sufetan Yansandan
Najeriya ya amince da nadin Ahmad Abdulrahman a matsayin sabon kwamishinan Yansandan jihar Kaduna, wanda ya canji mai barin gado, Austin Iwar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Kaakkain rundunar Yansandan jihar, Sabo Yakubu ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, 9 ga watan Agusta cikin wata sanarwar da ya fitar, inda yace Ahmad ya karbi ragamar iko tun a ranar 6 ga wata.
Shi dai Dansanda Ahmad ya kasance yana gudanar Tafsirin Al’Qur’ani a duk watan Azumin Ramadan a babban Masallaci dake shelkwatar rundunar Yansandan jihar Kaduna, inda yake fassara Al’Qur’ani da ilimi iya gwargwado.
An haifi Ahmad a garin Kirfi na jihar Bauchi, kuma ya shiga aikin Dansanda a shekarar 1990 bayan ya yi karatun digiri a jami'ar Usmanu Danfodiyo dake Sakkwato, sa'annan yayi karatun digiri na biyu a jami'ar jihar Kaduna.
A wani hira da aka taba yi da Ahmad, yace babban dalilin shigarsa aikin Dansanda shine tun bayan wani rikici da aka taba yin a Zangon Kataf a jihar Kaduna, inda yace Sojoji suka kama su ana wannan rikicn, basu sake suba har sai marigaygi Malam Abubakar Mahmud Gummi ya kwace su da kyar.
Ahmad yace bayan Malam ya kwacesu ne sai yake basu shawarar su shiga aikin Soja da Dansanda don su kare mutuncin addininsu, ya jaddada musu cewa da akwai masu a aikin ba za’a dinga ci musu mutunci ba, “Daga nan na yanke shawarar shiga aikin Dansanda.” Inji shi.
0 comments: