Thursday, 9 August 2018

Za mu ci gaba da yakar kama karya - Saraki

Shugaban majalisar dattawan Najeriya Bukola Saraki, ya sha alwashin cigaba da yaki da kama karya da kuma rashin gaskiyar dake gudana a karkashin gwamnati mai ci.


Saraki ya bayyana haka ne yayin ganawa da manema labarai bayan matakin da jami’an tsaron farin kaya suka dauka na tare hanyar shiga Majalisa.
Shugaban majalisar dattijan yace abin kunya ne yadda bangaren zartarwa ke amfani da jami’an tsaro wajen karan tsaye ga dokokin kasa.


A cewar Saraki, Najeriya kasa ce da ake sa rai sosai da shugabancinsu, wanda ya dace ace an hada karfi don cigaba a matsayin kasa amma sai aka jajirce wajen karya doka da nuna karfi ta hanyoyin da basu kamata ba.


A baya bayan nan Saraki ya mayar da martani ga masu kiran ya sauka daga mukaminsa ba shugabancin majalisar dattijai, bayan sauya shekar da ya yi zuwa jam’iyyar adawa ta PDP, inda ya ce manbobin majalisar ne suka zabe shi, don haka ba zai saurari duk wani matsin lamba ba.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

1 comment: