Monday, 27 February 2017

Mutane Hudu (4) Da Suke Hana Kowa Ganin Shugaba Buhari

Babu dai wanda ya isa ya ga shugaban kasar sai ta hannun su…
Idan ba Hajiya Aisha Buhari ko Osinbajo ba babu wanda ya isa ya ga Buhari.
A wani bincike da Jaridar Punch tayi an gano cewa wasu manyan kusoshi ne suka katange shugaba Buhari inda suka hana kowa ya gana da shi. Yanzu haka dai shugaba Buhari yana Landan kuma babu wanda ya isa ya je kusa da shi sai ta hannun wadannan mutane.

Ciki dai akwai shugaban Ma’aikatan gidan gwamnati da kuma wani mai taimakawa shugaban kasar watau Abba Kyari da kuma Tunde Sabi’u. Punch tace idan dai har ba Hajiya Aisha Buhari ko Mataimaki Yemi Osinbajo ba, babu wanda ya isa ya ga shugaba Muhammadu Buhari kai tsaye.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: