Tuesday, 25 July 2017

Shagali! Kun san kalar samfurin kamfutocin da za'a rabawa matasan N-Power?

Kawo yanzu dai shire-shire sun kusa kammala na gwamnatin tarayya da ke shirin bawa dukkan matasan da ke yin shirin nan na rage radadin talauci domin samun sauki wajen gudanar da ayyukan su. Hukumomin dake kula da shirin dai a farko sun shirya za su fara rarraba na'urorin ne a tsakiyar watan nan amma daga baya sai aka dan samu tsaiko aka dan daga zuwa nan gaba.
AREWARMU.com dai ta samu labarin cewa samfurin kwamfutocin da za'a rarraba din sun hada da ‘Tablets’ kaloli 8 da suka hada da Tablet kirar Afri-One (2-in 1), RLG Adulawo Limited, Samsung Tab E, Zinox Z Pad, Brain NPower IPAD, Techno Pad, Floss Signatures da Speedstar. Masu karatu dai zasu iya tuna cewa a karshen shekarar da ta gabata ne dai aka fara shirin nan na N-Power inda aka dauki matasa 200,000 a duk fadin Najeriya inda kuma gwamnatin tarayya ke biyan su N30,000 a duk wata.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: