Tuesday, 1 August 2017

An yi wani Barawo zigidir a kan ya saci wayoyin wuta [Video]

- Yan unguwar suna fama da matsalae sace-sace

- Da kyar dai wannan barawon ya fita da ran sa

- Gwamnati ta hana mutane daukan doka a hannu

Fusatattun matasa sun yiwa wani barawo dukan tsiya da kuma yi mushi tsirara bayan an kama shi da satan wayoyin lantarki a jihar Imo.
Mai laifin wanda ba a bayyana ainihin ko wanene ba, an kama shi ne a unguwan Umugoma dake cikin garin Imo.

A bayyanin da yan unguwan sukayi, sun ce sun dade suna fuskantar matsalolin sace-sace a unguwan ,saboda barayi na yawan fasa musu shaguna.

Barawon ya samu nasarar fita da ransa saboda yansanda sun zo daidai lokacin da matasan ke kokarin kuna shi.

Gwamnati ta dade ta yiwa mutane kashedi akan daukan doka a hannun su, musamman masu kona barayi idan suka ka masu. Wannan mumunan dabi’a kuma ya zama ruwan dare a Najeriya.

DOWNLOAD VIDEO NOW

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: