Tuesday, 1 August 2017

TIRKASHI: Kunji Barnar Da Barayi Sukai A Gidan Tsohon Shugaban Kasa Good luck Jonathan

- An shiga wani gida a Abuja na tsohon shugaban kasa Jonathan

- Jaridar PREMIUM TIMES su ka tabbatar da wannan labari.

Duk da haka, a cikin abin da ya bayyana mai karkatarwa,ba barayin da aka sani da sata su ka shiga gidan ba , amma jami'an tsaron da aka sanya su tsare gidan su suka shiga su kayi satan.

A Najeriya 'yan sandan sun kama jami'an tsaron da suka sata abubuwa mai daraja da dama wanda zasu kai miliyoyin naira daga Abuja mazaunin tsohon shugaban kasar.

'Yan sandan sun saci abubuwan ne daga gidan da yake a No. 89, Fourth Avenue a gundumar Gwarimpa da ke garin Abuja.

Sun hada da setin kujeru, tilbijin da dama, firji, su AC da akwatin-lodi na tufafi kamar zanen kara mai dauke da sunan tsohon shugaban kasar,kayan gargajiya na namiji da mace, yadin leshi da huluna.

PREMIUM TIMES na musamman sun tabbatar cewa jami'an 'yan sandan su uku suka gudanar da satar na tsawon watanni uku tun daga kusa Maris 2016, har sai da suka kaucewa kwashe komai da za'a iya fitarwa daga gidan, abin da suka sayar rarrabe zuwa dillalai a Panteka,kasuwar gwanjo, a tashar babbar mota, Gwarimpa.

Kakakin Mista Jonathan, Ikechukwu Eze, ya tabbatar da sata ma PREMIUM TIMES.
Ya kuma tabbatar da cewa an kama jami'an da abin ya shafa.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: