
- Mai Jaridar Sahara Reporters yace kudin da aka sata ya rikitar da Buhari.
- Irin satar da aka yi a Gwamnatocin baya dai ya wuce tunanin mutum Omoyele Sowore yace irin mahaukaciyar satar da aka rika tafkawa a Najeriya ya sa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kwanta rashin lafiya.
Mai Jaridar nan ta Sahara Reporters Omoyele Sowore ya bayyana wannan ne a wani taro da aka yi a Landan. Sowore yace yanzu haka ma an gama sace kudin Kasar don haka babu sauran satar da ake yi.
A wani taro da aka yi a Kent a karshen makon nan Sowore yace Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya kwanta ne lokacin da ya fahimci irin satar da aka buga a Najeriya. Yanzu dai Shugaban kasar ya fara murmurewa. Yanzu dai har Najeriya ta fita daga jerin kasashen da su ka yi kaurin suna wajen harkar cin hanci da rashawa a Duniya. Sowore yace dole Kasashen Duniya su taimaka wajen daina boye kudin sata daga Najeriya.
0 comments: