Daga Sagir Abubakar, Katsina
A wani labarin kuma, hukumar gidan rediyo ta Jihar Katsina ta yaba da irin gudummowar da kungiyoyin da ba na gwamnati ke bayarwa wajen bunkasa ilimin ‘yaya mata da wayar da kan jama’a a kan tsare-tsare da manufofin gwamnati.
Shugaban gidan rediyon Malam Sani Bala Kabomo ya yi yabon a lokacin da jami’an hadaddiyar kungiyar mata masu goyon bayan gwamnati gwamna Aminu Bello Masari suka kai masa ziyara.
Ya ce tashar rediyon za ta ci gaba da sheda wa jama’a irin ci gaban da gwamna Aminu Bello Masari ya samu ta hanyar aiwatar da ayyukan alkhairi a jihar.
Ya kuma bada tabbacin hada kai da kungiyoyin cigaban al’umma wajen kara wayar wa da jama’a kai a kan yad a za su zabi shugabanni nagari a zabuka masu zuwa.
Shugaban gidan rediyon ya bukaci cikakken hadin kan mambobin kungiyoyin domin cim ma burin da ta sanya a gaba.
Tunda farko shugabar kungiyar Hajia Zainab Abubakar wadda ta yi jawabi ta bakin PRO ta kungiyar Hajiya Jamila Abdullah,i ta ce kungiyar na shirya laccoci domin wayar wa mata kai game da muhimmancin ilimin ‘yaya mata tsaftataccen muhalli da kuma tsare-tsare da manufofin wannan gwamnati.
Hajiya Zainab Abubakar ta yaba wa hukumar gidan rediyo a kan yadda take kan gaba wajen yada manufofin wannan gwamnati. Haka nan kuma, shugaban gidan rediyon Katsina ya ce tashar za ta ci gaba da babban aikinta na shaida wa jama’a abubuwan da ke faruwa a ciki da wajen jihar.
Malam Sani Bala Kabomo ya fadi haka ne a lokacin da ya karbi jami’an reshen kungiyar muryar talaka na jihar Katsina.
Ya ce gidan rediyo na da muhimmanci ganin cewar yana ilimantarwa, da nishadantarwa da kuma wayar da kan jama’a.
Shugaban gidan rediyon ya bayyana godiya ga mambobin kungiya a kan ziyarar ganin cewar za ta kara dankon zumunci tsakanin gidan rediyon da kungiyar.
Tun da farko, mukaddashin shugaban kungiyar Kabir Shehu Yandaki ya ce ziyarar na da nufin godiya ga hukumar gidan rediyon a kan fayyacewa mutane gaskiya a kan ayyukan gwamnatin jihar.
Shugaban ya ce tashar gidan rediyon na ci gaba cikin sauri a saboda nada jami’ai masu hazaka domin su shugabanci gidan rediyon.
Sai dai ya bukaci lokaci a gidan rediyo domin gabatar da shirye-shirye ga jama’a.

0 comments: