Daga Khalid Idris Doya, Bauchi
Gwamnatin jihar Bauchi ta bayyana cewar tuni ta gayyato wata kungiyar kasa da kasa mai suna ALBASAR domin su duba lafiyar masu matsalar ciwon idanu a fadin jihar ta Bauchi. Sanarwar hakan na kumshe ne cikin wata sanarwa da mai tallafa wa gwamanan Bauchi kan fannin sadarwa Shamsuddeen Lukman Abubakar ya fitar a ranar Litinin 18 ga watan Satumbar 2017.
Shamsu ya ci gaba da cewa wannan shirin na cikin yunkurin gwamnatin jihar na inganta lafiyar al’umman Hihar Bauchi “A ci gaba da kokarin inganta sha’anin kiwon lafiya musamman ga masu karamin karfi, ne ya sa gwamnatin Jihar Bauchi karkashin jagorancin Mai Girma Gwamna, Barista Mohammed Abdullahi Abubakar ta gayyato babbar kungiyar nan ta kasa da kasa mai suna AlBASAR domin kula da lafiyan ‘yan Jihar masu fama da ciwon idanu”. In ji sanarwar
Lukman ya ce, ‘Albasar International Foundation’ sun yi fice wurin samar da kiwon lafiya wanda ya shafi idanu kasancewar su kungiya wacce ta tara kwararru kuma hazikan likitocin ido daga sassa daban-daban na duniya, a bisa wannan dalilin ne gwamnatin ta gayyato kungiyar domin yin aiki kan jama’a masu fama da cutar idonu domin a yi musu aiki kyauta ba tare da biyan sisin kwabo ba.
A bisa haka ne sanarwar ta yi kira ga dukkanin dan jihar Bauchi da ke fama da wannan matsalar na ciwon ido da ya garzaya babban kwararru da ke Baucin domin amfana da shirin “A madadin Gwamnatin Jihar Bauchi muna kira ga duk ‘yan Jihar wadanda su ke fama da matsalar da ta shafi ido da su garzaya zuwa babban asibiti na Specialist (BACAS) domin samun kulawa ta musamman kyauta daga wurin kwararru kan harkar lafiyar ido”. In ji sanarwar
Sanarwar ta ce za a fara wannan shirin gudanar da aikin ne daga ranar Alhamis 21 ga wannan watan Satumbar 2017. A bisa haka ne gwamnatin ta bukaci masu ciwon su hanzarta don neman lafiyarsu.
Gwamnan ya yi fatan Allah ya ba kowa lafiya “Muna fatan Allah ya sa a yi aikin a gama lafiya, sannan kuma Allah ya baa kowa da kowa lafiya”.

0 comments: