Thursday, 9 August 2018

Katafaren Hotunan Fadar Shugaban Kasar Nigeria Wanda Aka Fi Sani Da Villa

Ko shakka babu inda mutum ya kwana ya kuma tashi a kasar nan to tabbas ya san da inda ake kira fadar shugaban kasa, ko kuma 'Villa' a turance.

Fadar shugaban kasar dai, ga wadanda basu sani ba tana a garin Abuja ne babban birnin tarayya a wata unguwa da ake kira Aso Rock a rukunin fadar mulki ta Three Arms Zone da ta kunshi majalisun tarayya, da kuma bangaren shari'a.
Tabbas an kawata wurin sosai don duk wanda ka tambaya wanda ya san wurin zai tabbatar maka da hakan.

Tarihi dai ya tabbatar mana da cewa da fadar mulkin kasar tana a garin Legas ne kafin daga bisani gwamnatin Janar Babangida ta maido ta a inda take yanzu.

AREWARMU.com dai ta tattaro maku wasu daga cikin hotunan fadar domin wadanda ma basu taba zuwa ba su kashe kwalkwatar idon su.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: