Saturday, 11 March 2017

Tsakanin Hameed Ali da Sanatoci: Ba’a nada ni shugaban Kwastam don saka Unifom ba

Shugaban hukumar Kwastan Hameed Ali ya ce ba an nada shi shugaban hukumar kwastam bane don ya dunga saka Uniform.
Majalisar Dattijai sun bukaci Hameed Ali da ya zo gabanta domin amsa wadansu tambayoyi kan tilastawa masu shigo da motoci ta iyakokin Najeriya da yin rijista da hukumar da kuma wadansu abubuwan da hukumar ta keyi da bai gamsar dasu ba.
Hameed Ali yace an nada shi ne domin yayi aiki ba yawo da Unifom ba.
Shugaban hukumar kwastam din ya fadi hakanne a wata hira da yayi da gidan talabijin na TVC inda ya maida wa majalisar Dattijai martini kan gaiyatarsa da sukayi da yazo gabanta amma fa sanye da Uniform din Kwastam.
Yace abinda ya kamata su majalisar su matsa domin sani shine irin aiyuka da nasararin da ake samu a hukumar tun bayan ya zama shugaban hukumar ba saka unifom ba.
Yace baya tsoron fuskantarsu amma fa hakan zai yiwu ne idan aka samu jitua da fahimtar juna a tsakaninsu.
“ Abin da ya kamata su sa ido akai shine, shin ina yin aikin ko A’a.”
“Har yanzu ban ga takardan gaiyatarsu baa mm idan har suka bi ta hanyar da ya kamata, wato hanyar da ake bi domin gaiyatar jami’in gwamnati, tabbas zan amsa gaiyatar.”

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: