Saturday, 2 September 2017

Karanta ka karu: Ko kun san Jihar da ta fi yawan ma'aikatan gwamnatin tarayya a Najeriya?

Gwamnatin tarayya ce gaba a bangaren samar da ayyuka a kasa. Duk lokacin da gwamnatin tarayya za ta dauki aiki ta kan yi raba dai-dai ne tsakanin jihoshin Najeriya. A wata kididdiga da tsohon shugaban sashen kula da bunkasa ayyukan gwamnatin tarayya, Dakta Joe Abah, ya fitar ta nuna adadin jimillar ma'aikatan gwamnatin tarayya da ke karkashin ma'aikatun tarayya da kuma kason da kowacce ke da shi.

Ga adadin ma'aikatan da kowace jiha ke da su da kuma jimillar ma'aikatan kamar yadda Joe Abah ya wallafa;

Jihar Imo 5825, Jihar Kogi 5186, Jihar Ogun 4669, Jihar Delta 4419, Jihar Akwa Ibom 4416, Jihar Benue 3951, Jihar Edo 3890, Jihar Abia 3579, Jihar Anambra 3576, Jihar Kaduna 3199, Jihar Ondo 3393, Jihar Oyo 3244, Jihar Osun 3321, Jihar Enugu 2695, Jihar Cross River 2681, Jihar Ekiti 2613, Jihar Plateau 2542, Jihar Kwara 2537, Jihar Niger 2193, Jihar Lagos 2180, Jihar Borno 1822, Jihar Adamawa 1727, Jihar Rivers 1675


Jihar Kano 1545, Jihar Nasarawa 1452, Jihar Katsina 1237, Jihar Gombe State 1218, Jihar Bauchi 1172, Jihar Taraba 1112, Jihar Bayelsa 957, Jihar Kebbi 875, Jihar Ebonyi 865, Jihar Yobe 744, Jihar Sokoto 732, Jihar Jigawa 675, Jihar Zamfara 543, san nan sai wasu mutum 518 da ba a tantance jihoshin da suka fito ba. Jimillar ma'aikatan ya kama 89,511.

Yankin kudu maso gabas na da kaso 18.47% na yawan ma'aikatan, sai yankin kudu maso kudu da kaso 20.15%, san nan kudu maso yamma na da kaso 21. 69%, a yayin da arewa ta tsakiya ta samu kaso 19.95%, arewa maso gabas tana da kaso 10.44%, sai arewa maso yamma da kaso 9.83%.

Source: Naij.com Hausa

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: